18 Satumba 2021 - 12:15
Iran Ta Zama Mamba Na Dindindin A Cikin Kungiyar SCO

An bude taron kasashen kungiyar SCO ko Shanghai Cooperation Organization karo na 21 a birnin Dushambe na kasar Tajakisatn, inda shugaban kasar Cana Xi Jinping ya fadawa taron cewa kungiyar ta karbi kasar Iran a matsayin mamba na dindindin a cikinta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kungiyar SCO dai mai kasashe 8 tabbatattu da kuma kasashe 4 masu sanya ido ta bude taronta na 21 ne tare da halattar shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi, sanna shugaban kasar Cana ya gabatar da jawabinsa na kafar bidiyo.

Sauran shuwagabannin kungiyar ta suka sami halattan taron sun hada da na Tajakistan, Kyrqizistan, Kazakistan, Belarus, Pakistan, Turkmenistan, da kuma Uzbekistan.

Har’ila yau kasashen Masar Qatar da kuma Saudiya suna da matsayin yan kallo a kungiyar. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya na fada a jawabinda da ya gabatar a taron kan cewa al-amuran al’adune suka fi zama abinda ya hada kasashen na SCO, kuma daga nan yakamata kasashen su fara aiki tare.

342/